El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019

El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben 2019

- El-Rufai yayi alkawarin mara wa Buahri a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2019

- Yan APC akida sun yi alkawarin hana APC jihar Kaduna tsayar da Elrufai kadai a matsayin dan takarar gwama a 2019

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa, shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna sun yanke shawarar mara wa shugaban kasa Muhammadu baya a zaben 2019.

El-Rufai ya bayyana haka ne a wata taro da gwamnatin jihar Kaduna ta hada a ranar Asabar.

Anyi taron ne saboda shiryeshiryen gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2018.

El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019

El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019

El-Rufai Ya ce: “Yan Kaduna da shugabannin jam’iyyar jihar suna bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, da ikon Allah Buhari zai samu nasara.

KU KARANTA : Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

“Ina rokon ku da ku cigaba da yi wa shugaban kasa adu’a, Allah ya ba shi lafiya da karfin jiki, saboda ya cigaba da shugabancin sa na adalci.

Bayan haka wasu daga cikin yayan jam’iyyar APC da ke kiran kan su APC akida sun yi alkawarin hana jam’iyyar su tsayar da El-Rufai a matsayin takarar gwamna jihar shi kadai a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel