Kungiya ta shigar da gwamnatin tarayya kara a kan cigaba da biyan tsofin gwamnoni albashi a matsayin sanatoci da ministoci

Kungiya ta shigar da gwamnatin tarayya kara a kan cigaba da biyan tsofin gwamnoni albashi a matsayin sanatoci da ministoci

- Kungiyar ta ce ta shigar da karar ne bisa gazawar gwamnati na daina biyan tsofin gwamnonin

- Sun bukaci tsofin gwamnonin su mayarwa gwamnati biliyan 40 da suka karba a matsayin albashi

- Kotu bata saka ranar da zata fara sauraron karar ba

Kungiyar SERAP mai rajin yaki da almundahana da cin hanci a Najeriya ta shigar da gwamnatin tarayya kara gaban wata babbar kotu a Legas bisa abinda kungiyar ta kira gazawar gwamnati wajen dakatar da biyan tsofin gwamnonin albashi a matsayin sanatoci da ministoci alhalin suna karbar fansho a matsayin tsofin gwamnonin.

Kungiya ta shigar da gwamnatin tarayya kara a kan cigaba da biyan tsofin gwamnoni albashi a matsayin sanatoci da ministoci

Kungiya ta shigar da gwamnatin tarayya kara a kan cigaba da biyan tsofin gwamnoni albashi a matsayin sanatoci da ministoci

Kungiyar ta bayyana cewar a cikin karar data shigar gaban kotun, tana zargin gwamnatin da kasa karbo naira biliyan 40 da tsofin gwamnonin suka karba a matsayin albashi ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban kungiyar, Timothy Adewale, da kungiyar ta fitar a yau ta ce gwamnatin tarayya ce kadai keda ikon takawa tsofin gwamnonin birki. Kungiyar ta kara cewar; "Ya zama dole mu shigar da karar gwamnatin tarayya domin a baya mun aike da takardar koke ga ministan shari'a kuma babban mai shigar da kara a madadin gwamnati, amma har ya zuwa yanzu ba a dauki wani mataki ba".

DUBA WANNAN: Hadarin tankar man fetur ya yi sanadin mutuwar mutum 5 da konewar ababen hawa masu yawa a Kaduna

Saidai a wani rahoto na daban, Ministan ma'adanai kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, Ministan kwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige, da kuma ministan aiyuka, gidaje, da lantarki, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola, sun musanta karbar tudu biyu na kunshin kudaden albashin.

Kotu bata saka ranar fara sauraron karar da Kungiyar SERAP ta shigar ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel