Sabon salo: PDP za ta samar wa mata masu sha’awar takara kyautar fom

Sabon salo: PDP za ta samar wa mata masu sha’awar takara kyautar fom

- Jam'iyyar PDP a jihar Delta ta ce mata masu sha’awar takara a kananan hukumomi za su samu kyautar fom

- Jam'iyyar ta yanke wannan shawara domin karfafa mata masu sha’awar takara a jihar

- Shugaban PDP ya bayyana cewa za a fitar da ‘yan takarar kananan hukumomi a wannan watan

Jam'iyyar PDP a jihar Delta ta bayyana cewa za ta samar wa mata wadanda ke sha’awar takara kyautar fom a zaben kananan hukumomin da za a gudanar a shekara ta 2018 a jihar.

Jam'iyyar ta ce, ta yanke wannan shawara ne domin karfafa mata masu sha’awar takara a jihar don shiga harkokin siyasa.

NAIJ.com ta tattaro cewa, jam’iyyar ta kafa kudin sayar fom ga maza wadanda ke neman takarar shugabancin kananan hukumomin a matsayin naira miliyaran 1 da kuma naira dubu 200 ga masu neman takarar kansila.

Sabon salo: PDP za ta samar wa mata masu sha’awar takara kyautar fom

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP, sanata Ahmed Makarfi

Da yake jawabi a taron manema labarai a Asaba a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Kingsley Esiso, ya bayyana cewa jam'iyyar ta ba da umarni ga duk kanannan hukumomi cewa su kebe akalla kujeru 3 na kansila ga mata masu sha’awar takara a fadin jihar.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta zargi gwamna Nyesom Wike da daukar nauyin yiwa 'yan sanda zanga-zanga a jihar Ribas

Esiso ya bayyana cewa za a fitar da ‘yan takarar kananan hukumomi a wannan watan kafin zabe wanda za a yi a ranar 6 ga watan Janairu, 2018 .

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel