Sojojin Najeriya sun fasa Neja-Delta da Operation crocodile smile II

Sojojin Najeriya sun fasa Neja-Delta da Operation crocodile smile II

- Sojin Najeriya ta aika Runduna ta musamman zuwa Neja-Delta

- Rundunar Operation crocodile smile II sun shiga Yankin kasar

- Sojojin su na kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin kasar

Za ku ji cewa duk da gargadin da Kasar Amurka ta yi Najeriya, Sojojin Najeriya sun aika Runduna ta musamman zuwa Yankin Neja-Delta mai arzikin mai.

A jiya Rundunar Sojin kasar ta bakin Manjo Janar Enobong Udoh ta sanar da cewa ta aika Sojoji na musamman na tawagar Operation crocodile smile zuwa Jihohi 6 na bangaren Neja-Delta domin kawo karshen tsageranci a Yankin na Jihohin Ribas, Bayelsa da sauran su.

KU KARANTA: Amurka na gargadin Najeriya game da amfani da Sojojin yaki

Janar Udoh ya bayyana cewa manufar Sojojin ita ce tsaida harkar tsageranci da kuma takawa masu garkuwa da mutane burki a Yankin. Janar din ya bayyana cewa mutanen gari su yi aiki ko kasuwancin su ba tare da wani dar-dar ba don kuwa burin su zaman lafiya.

Rundunar Sojin kasar za ta hada kai ne da sauran Jami’ai irin su FRSC, NSCDC da kuma Jami’an kwastam da na gidan yari da sauran su. Amurka dai ta gargadi Shugaba Muhammadu Buhari ya guji amfani da karfin Soji wajen shawo kan rikice-rikicen kasar da ake fama da su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel