Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

- Ana zargin wani jami’in dan sanda a jihar Kaduna da harbin wata budurwa saboda taki amince da soyayyarsa

- Buduruwar ta kasance daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Sha’awa ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya harbe ta

Ana zargin wani jami'in dan sanda a Kaduna da harbin wata budurwa da bindiga saboda taki amincewa da soyayyarsa.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito budurwar mai suna Sha’awa Nasiru, mai kimanin shekaru 20 da haihuwa daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Majiyar ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya hangi sha’awa ta shiga wani gida, yayin da take fitowa sai ya kira sunanta, tana amsawa zai ya saka mata harsashi.

Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

Budurwar da aka harbe a kan so

Nan da nan mutane suka watse a guje sakamakon jin harbin bindigar kafin daga bisani wasu suka garzaya inda budurwar take a kwance cikin jini suka dauke ta zuwa asibitin Doka dake jihar Kaduna, amma abin yafi karfinsu, inda suka ce a mika ta zuwa babban asibiti, sai dai hakan bata samu ba sabida yajin aikin da kungiyoyin ma’aikatan lafiya suke yi, ciki kuwa har da asibitin koyarwa dake Gwagwalada.

KU KARANTA: Sojoji sun yi wa wasu 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe biyu

Wata kawar ta mai suna Salamatu Sani ce ta shaidawa wa majiyar mu cewa, “Sha’awa ta shaida wanda ya harbe ta a lokacin da suka iso wajenta cikin gaggawa, a inda ta shaida cewar ‘insfekto ne' ", inji kawar ta.

Sai dai duk yunkurin da majiyar tamu tayi don jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu abun yaci tura domin yaki amsa kiran kuma yaki maido da sakon tes da akayi masa kan batun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel