An yankewa wani Dan wasan Real Madrid hukuncin dauri a gidan kurkuku

An yankewa wani Dan wasan Real Madrid hukuncin dauri a gidan kurkuku

– Tsohon Dan wasan Real Madrid Ricardo Carvalho ya ga ta kan sa

– An samu Dan wasan da rashin gaskiya wajen harkar biyan haraji

– A sa’ilin da Dan kwallon yake taka leda a Sifen ya aikata laifin

Mun ji labari daga Jaridun Turai cewa an samu wani Dan wasan kasar Portugal da rashin gaskiya wajen harkar biyan haraji.

An yankewa wani Dan wasan Real Madrid hukuncin dauri a gidan kurkuku

Laifin haraji ya sa an aika Carvalho gidan yari

Yanzu haka tsohon Dan wasan bayan Kungiyar Real Madrid Ricardo Carvalho ya ga ta kan sa bayan da aka yanke masa hukuncin dauri a gidan maza na watanni 7 bayan ya tabbatarwa da Kotu cewa bai da gaskiya.

KU KARANTA: Messi da Ronaldo su na cikin barazanar zuwa Gasar Duniya

Dan wasan ya furtawa Kotu da bakin sa cewa ya aikata laifin da ake zargin sa da shi na kin biyan wasa kudin haraji na sama da fam rabin Miliyan na Euro a lokacin da yake buga kwallo a Madrid daga shekarar 2011 zuwa 2013.

Haka kuma an ci ‘Dan wasan da yanzu yake taka leda a Kasar Sin tara na sama da fam 140,00. Sai dai tun da wannan ne karo na farko da aka samu ‘Dan kwallon da laifi da kyar zai yi zaman kaso. Ana dai zargin wasu ‘Yan wasan na Real Madrid da kin biyan haraji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel