Hadarin tankar man fetur ya yi sanadin mutuwar mutum 5 da konewar ababen hawa masu yawa a Kaduna

Hadarin tankar man fetur ya yi sanadin mutuwar mutum 5 da konewar ababen hawa masu yawa a Kaduna

- A kalla hadarin yayi sanadin mutuwar mutum 5

- Da yawa da suka jikkata na asibiti

- Motoci da dama dake ajiye gefen hanya sun kone

A kalla mutum biyar ne suka rasa ran su ranar asabar bayan wata tanka makare da man fetur tayi bindiga a Tafa dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Hadarin tankar man fetur ya yi sanadin mutuwar mutum 5 da konewar ababen hawa masu yawa a Kaduna

Hadarin tankar man fetur ya yi sanadin mutuwar mutum 5 da konewar ababen hawa masu yawa a Kaduna

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa gidan talabijin na "Channels" cewar, motar dake makare da kalanzir na kokarin kaucewa rami ne a kan hanya lokacin data kwace daga hannun direban kuma ta kama da wuta bayan ta fadi.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta zargi gwamna Nyesom Wike da daukar nauyin yiwa 'yan sanda zanga-zanga a jihar Ribas

Wasu mutum biyu an ce sun mutu ne bayan shake su da hayakin man ya yi, sannan wasu mutum uku sun kone kurmus har lahira.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA, Yushau Shuaib, ya tabbatar da afkuwar hadarin, saidai yace bashi da masaniya ko hadarin ya jawo rasa rayuka.

Rahotanni dai sun nuna cewar da yawa daga cikin wadan da suka jikkata na karbar magani a asibiti, sannan motoci da yawa dake ajiye gefen titi sun kone kurmus.

Babbar Hanyar ta Abuja zuwa Kaduna ita ce ta hada arewacin Najeriya da babban birnin Abuja sannnan ta wuce zuwa jihar Kogi zuwa kudancin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel