Jeddah: Wani dan bindiga ya kai hari kan fadar sarkin Saudiyya, ya kashe masu tsaro 2

Jeddah: Wani dan bindiga ya kai hari kan fadar sarkin Saudiyya, ya kashe masu tsaro 2

- An kai hari a kan fadar Salman na sarkin Saudiyya yayin da aka halaka masu tsaron gida guda 2 da kuma jikkata wasu 3

- Ma'aikatar cikin gida ta bayyana cewa an kai harin ne a bakin kofar shiga fadar a ranar Asabar

- Ofishin jakadancin Amurka a Saudi Arabia ta gargadi 'yan ƙasar game da harin tun farko

Wani dan bindiga ya kai hari a kan fadar Salman na sarkin Saudiyya wanda ke Jeddah yayin da ya harbe wasu masu tsaron gida guda 2 da kuma jikkata wasu 3.

Ma'aikatar cikin gida ta bayyana cewa an kai harin ne a bakin kofar shiga fadar a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, jami'an tsaron gida a fadar sun kashe dan bindigar, wanda ma'aikatar ta gano a matsayin dan kasar Saudiyya mai shekaru 28 da haihuwa wanda yake rike da bindigar Kalashnikov da gurnati 3.

Jeddah: Wani dan bindiga ya kai hari kan fadar sarkin Saudiyya, ya kashe masu tsaro 2

Sarkin Saudiyya, Salman Ibn Abdulaziz

Ofishin jakadancin Amurka a Saudi Arabia tun farko ta gargadi 'yan ƙasar game da harin.

KU KARANTA: An yi an gama: Donald Trump yace Amurka ba za ta nemi tattaunawa da Koriya ba

"Saboda ayyukan 'yan sanda a yankin, an shawarci ‘yan kasar Amurka su yi taka tsantsan a lokacin da suke tafiya a yankin", in ji ofishin jakadancin a cikin wata taƙaitaccen bayani.

Wannan gargadin ta zo ne bayan da 'yan sanda na Saudiyya suka kai hari a kan inda wasu ‘yan 'ta'adda ke boyewa wadanda aka danganta da kungiyar ISIS a wannan makon, inda suka kashe mutane 2 da kama wasu 5, a cewar hukumar tsaro ta kasa.

Tun daga farkon shekara ta 2014, kungiyar IS ta dauki nauyin harbe-harbe a kan 'yan Shi'a da jami'an tsaro a kasar.

Saudi Arabia tana cikin membobin kungiyar hadin gwiwar kasashen duniya wanda Amurka ke jagoranta wajen yaki da kungiyar 'yan ta'addan Sunni a Syria da Iraki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel