Jam'iyyar APC ta zargi gwamna Nyesom Wike da daukar nauyin yiwa 'yan sanda zanga-zanga a jihar Ribas

Jam'iyyar APC ta zargi gwamna Nyesom Wike da daukar nauyin yiwa 'yan sanda zanga-zanga a jihar Ribas

- Jam'iyyar ta ce shi yake biya tare da ingiza masu zanga-zangar

- Gwamnatin jihar ta musanta zargin

- Dimbin matasa a jihar Ribas na zanga-zangar nuna adawa da aiyukan 'yan sanda masu yaki da fashi da makami

Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta bayyanawa duniya cewar gwamna Nyesom Wike ne ke daukan nauyin zanga-zangar da wasu matasa ke yi a jihar ta nuna adawa da aiyukan 'yan sanda masu yaki da fashi da makami, wato SARS. Jam'iyyar ta bayyana wannan zargi ne ta bakin sakataren ta na yada labarai a jihar Ribas, Cif Chris Finebone. Cif Chris ya bukaci gwamnan da ya daina yaudarar jama'a.

Jam'iyyar APC ta zargi gwamna Nyesom Wike da daukar nauyin yiwa 'yan sanda zanga-zanga a jihar Ribas

Gwamna Nyesom Wike

Saidai gwamnatin jihar Ribas ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar, Emma Okah, ta musanta wannan zargi na jam'iyyar APC, tare da bayyana cewar gwamnatin Wike na kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama'a ne kawai.

DUBA WANNAN: Bincike: Shin cin ganda na da wata fa'ida ga lafiya?

Jam'iyyar APC na zargin cewar gwamna Wike na daukan nauyin zanga-zangar ne domin yakar kwamandan rundunar 'yan sanda ta SARS saboda yaki amincewa gwamnan ya yi magudi a zaben da aka maimaita a jihar tun watan Disambar shekarar data gabata. Jam'iyyar ta ce gwamna Wike bai kamata yake karya tare da saka siyasa cikin harkar tsaro ba.

A ranar juma'a dandazon matasa dauke da takardu masu rubuce da sakonni sun yi zanga-zanga domin nuna adawar su da aiyukan'yan sanda masu yaki da fashi da makami wato SARS.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewar gwamna Wike na son ganin kwamandan na SARS ya bar jihar ta kowacce hanya musamman ganin shekarar zabe ta 2019 na kara matsowa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel