Russia 2018: Kasashe 12 da su ka samu kai wa Gasar cin Kofin Duniya

Russia 2018: Kasashe 12 da su ka samu kai wa Gasar cin Kofin Duniya

- Najeriya ta isa Gasar cin kofin Duniya da za a buga a 2018

- Super Eagles ce ta farko da ta samu zuwa Gasar a Afrika

- Kasashen Duniya irin su Portugal, Argentina su na cikin rudu

Za ku ji cewa Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ce ta farko da ta samu zuwa Gasar cin kofin Duniya daga Nahiyar Afrika.

Russia 2018: Kasashe 12 da su ka samu kai wa Gasar cin Kofin Duniya

Kungiyar Super Eagles ta isa Gasar World Cup

Manyan ‘Yan wasan Duniya irin su Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina su na cikin rudu domin har yanzu kasashen su ba su kai labari ba. Haka ma dai irin su Kasar Faransa su na da sauran aiki.

KU KARANTA: Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta a wasan Zambia

Kasashe 12 ne dai su ka samu kai wa Gasar cin Kofin Duniya da za a buga a kasar Rasha a shekarar 2018. Kasashen sun hada da:

Rasha

Brazil

Mexico

Iran

Japan

Koriya ta Kudu

Saudi Arabia

Jamus

Ingila

Sifen

Beljium da

Najeriya

Dan wasan nan na Arsenal Alex Iwobi ne dai ya zura kwallon daga shigowan sa wasan a raga a minti na 75 wanda ya ba Najeriya nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel