Biyafara: Al’ummar yankin Abiya sun koka game da bacewar Kanu da iyayensa

Biyafara: Al’ummar yankin Abiya sun koka game da bacewar Kanu da iyayensa

- Al’ummar Afaraukwu da ke yankin karamar hukumar Umuahia sun koka game da bacewar Nnamdi Kanu da iyayensa

- Al'ummar sun bayyana cewa mutanen 3 sun bace bayan harin da aka kai garin a watan Satumba 10

- Mutanen yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Abiya da na tarayya don yin bincike ko sojoji sun tafi da su

Shugabannin gargajiya na al’ummar Afaraukwu da ke yankin karamar hukumar Umuahia ta arewa na jihar Abiya sun yi kira ga gwamnatin jihar don taimaka musu wajen neman shugaban kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu da iyayensa.

Sun koka cewa Kanu da mahaifiyarsa da kuma ubansa, wanda shi ne sarkin garin, sun bace bayan harin da aka kai garin Kanu a watan Satumba 10.

A cewar su, bacewar Eze Israel Kanu da matarsa da kuma dansa fiye da makonni 3 bayan harin sojoji ya kasance abin damuwa gare su.

Biyafara: Al’ummar yankin Abiya sun koka game da bacewar Kanu da iyayensa

Shugaban kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu

Wani daga cikin ‘yan majalisar fadar sarkin, Chimechefulam Odoemelam, ya bayyana wa majiyar NAIJ.com cewa yana matukar damuwa game da bacewar sarkin da iyalansa.

KU KARANTA: Biyafara ba ta cikin ajandan iyan kabilar Igbo – Inji Ohanaeze

Ya ce, "Gaskiyar ita ce, ba mu ji daga sarkinmu tun lokacin da muka dawo. Kowa ya damu da wannan batun domin ba mu san inda za mu iya neme shi ba”.

Odoemelam ya yi kira ga gwamnatin jihar Abiya da na tarayya don bincikar sojojin da suka mamaye fadar sarkin ko sun tafi da mutanen.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel