An yi an gama: Donald Trump yace Amurka ba za ta nemi tattaunawa da Koriya ba

An yi an gama: Donald Trump yace Amurka ba za ta nemi tattaunawa da Koriya ba

- Shugaban kasar Amurka yace an gama sulhu da Kasar Koriya

- A cewar sa an yi kokarin sasantawa amma ba a ci nasara ba

- Donald Trump yace Gwamnatocin baya sun yi kuskure

Mun samu labari daga Jaridar Guardian cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump yace an gama sulhu da Kasar Koriya ta Arewa.

An yi an gama: Donald Trump yace Amurka ba za ta nemi tattaunawa da Koriya ba

Shugaba Donald Trump na Amurka

A cewar Shugaban kasar duk wani yunkuri da aka yi a baya na zaman tattaunawa da kasar bai kai ko ina ba don haka Shugaban yake ganin cewa abu daya kurum ya rage. An dai dade ana ta ce-ce-ku-ce tsakanin Shugaban kasar na Amurka da kuma na kasar Koriyar.

KU KARANTA: Amurka da ja kunnen Gwamnatin Shugaba Buhari

Trump ya zargi Gwamnatocin Barack Obama da sauran su da rashin yin abin da ya dace wajen kawo karshen wutar rikicin tuni tuni. Trump dai yace Sakataren Gwamnatin kasar na bata lokacin sa ne ma da yake kokarin zama da kasar ta Koriya ta Arewa.

Kwanakin kun ji cewa Shugaba Robert Mugabe yayi kira ga Shugaban kasar ya nemi a zauna lafiya a Duniya ba tare da an tada fitina ba. Mugabe ya soki yadda Shubaban kasar Amurka Trump ya rika barazanar tada wutar yaki ga wasu kasashen Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel