Ba komai ne ake amfani da karfin Soji ba – Amurka ta fadawa Buhari

Ba komai ne ake amfani da karfin Soji ba – Amurka ta fadawa Buhari

- Kasar Amurka ta kira Shugaban kasa Buhari ya nemi a sasanta

- Amurka tace ba fa komai bane ake amfani da karfin kan bindiga

- Kasar ta kuma yi kira da a binciki asalin sababin matsalolin kasar

Za ku ji cewa Kasar Amurka ta kira Shugaban Najeriya Buhari ya nemi kawo karshen rikicin kasar ne ta lalama ba ta karfin Soji ba.

Ba komai ne ake amfani da karfin Soji ba – Amurka ta fadawa Buhari

Amurka ta fadawa Buhari ya nemi zaman lafiya

Mun samu labari cewa kwanaki Kasar Amurka ta kira Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya bi a sannu wajen shawo kan rikice-rikicen kasar da ake fama da su. Yanzu haka ana fama da ‘Yan bangaren su Biyafara a Najeriya.

KU KARANTA: An caccaki Shugaban Amurka Donald Trump

A wani taro da Cibiyar USIP ta neman zaman lafiya na kasar Amurka ta gudanar a Garin Washington an kira Gwamnatin Buhari da ke fama da rikicen Boko Haram da sauran su da ta tattauna da masu kokarin tada rikici a kasar domin kawo zaman lafiya.

Gwamnatin Kasar dai ta baza Rundunar Sojoji a Yankin kudu maso gabashin kasar inda ake kukan Biyafara wanda hakan ya jawo aka fara magana a Duniya. Kasar ta Amurka tayi kira da a binciki asalin sababin matsalolin idan har ana so a shawo karshen rikicin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel