Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

- Alhaji Abubakar ya ce Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsin tattalin arzikin idan gwamnatin ba ta rage kashe kudade ba

- Tsohon ministar ya ce kara jihohi a kasar ba zai kawo karshen kabilanci ba

- Abubakar ya ce mulkin bangarance kadai zai kawo karshen matsalar koma baya tattalin arziki a Najeriya

Wani tsohon ministar kudi, Alhaji Abubukar Alhaji, yace Najeriya za ta cigaba da fuskantar koma bayan tattalin arziki, idan gwamnati ba ta dauki matakin rage kashe kudade ba.

Alhaji, wanda ya kasance masanin tattalin arziki kuma tsohon sekatare na dindindin, ya fadi haka ne a wata zanatawa da yayi da yan jaridar Sun, inda yace mulkin bangaranci kadai zai ceci Najeriya daga matsalar koma baya tattalin arziki da ta ke fuskanta.

Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

Dalilin da yasa Najeriya za ta cigaba da fuskantar matsalar koma bayan tattalin arziki - Abubakar

Tsohon ministar, kuma sardaunar Sokoto, yace kara samar da jihohi a kasar ba zai kawo karshen matsalar kabilanci ba.

KU KARANTA : An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano

“Idan aka rage kashe kudade a kasar, Najeriya za ta fita daga koma bayan tattalin arziki.

“Babu yadda za a yi mu fita daga koma bayan tattalin arziki bayan muna da gwamnoni 36, kuma ko wani jiha ta da kwamishinoni 36 ko sama da haka.

“Kusan sama da rabin kudaden shiga a kasar, ana amfani ne da su ne wajen kula da manyan jami'an gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel