Patience Jonathan ta kasance mai girman kai da mummunan hali – Inji tsohon jakadan Amurka

Patience Jonathan ta kasance mai girman kai da mummunan hali – Inji tsohon jakadan Amurka

- Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya ya ce uwargidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tana da girman kai da mummunan hali

- Jakadan ya ce abin mamaki ne yadda matar Jonathan ta mallaki dala miliyan 35

- Campbell ya ce akwai zargin cewa Buhari na amfani da EFCC don ya yaki abokan gaba na siyasa

Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya bayyana uwargidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Patience, a matsayin mai girman kai da mummunan hali a lokacin da ta kasance uwargidan Najeriya.

A wani bangare da ya rubuta a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba wanda ya gabatar a shafin yanar gizon na hukumomin harkokin waje, Campbell ya yi mamakin yadda matar Jonatan ta kasance mai arziki bayan da ta yi amfani da mafi yawan rayuwarta a matsayin ma’aikacin gwamnati.

Abin mamaki ne bayan da ta shafa mafi yawan rayuwarta a matsayin ma’aikaci gwamnati za ta iya tara makuddan kudi na dala Amurka miliyan 35.

Patience Jonathan ta kasance mai girman kai da mummunan hali – Inji tsohon jakadan Amurka

Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell

Idan dai baku manta ba NAIJ.com ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC tana bincike matar Jonathan kuma ta rufe wasu asusun ajiyar banki hudu na ta, yayin da aka kwace wasu dukiyarta.

KU KARANTA: Kasancewa a harkokin siyasa ya kai ni ga talauci – Inji Obi

Da yake jawabi game da yaki da cin hanci da rashawa na shugaba Muhammadu Buhari, Campbell ya ce, "Akwai babban kalu bale ga yaki da cin hanci da rashawa na shugaba Buhari, musamman a tsakanin 'yan jam’iyyar adawa ta PDP. Wasu sun ce Buhari na amfani da EFCC don ya yaki abokan gaba na siyasa. A wasu yankunan da Krista suka fi rinjaye a kasar ana ta gunaguni cewa yaki da cin hanci da rashawa wani ɓangare na kokarin fifita musulmi akan Kiristoci.

A cewarsa, akwai al'ada a Najeriya na shugabannin da ke amfani da hukumar EFCC da sauran hukumomin cin hanci da rashawa a kan abokan gaba na siyasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel