2019: Babu abin da zai hana mu cin zabe Inji Osinbajo

2019: Babu abin da zai hana mu cin zabe Inji Osinbajo

- Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ce APC za tayi nasara a 2019

- A cewar sa babu abin da zai hana Jam'iyyar lashe zabe mai zuwa

- Osinbajo yace gyara su ka zo yi kuma ana yi sai dai abin babu sauki

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wadanda za su lashe zaben 2019 wanda yace ba shakka Jam'iyyar su ce ta APC.

2019: Babu abin da zai hana mu lashe zabe Inji Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo tare da Shugaba Buhari

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ce ba abin da zai hana Jam'iyyar APC mai mulki nasara a zabe mai zuwa lokacin da yake amsa tambaya daga wani Dan Jaridar Channels TV. Osinbajo yace babbar matsalar kasar nan ita ce yaki da rashin gaskiya wanda ake kokarin tsaidawa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta samawa matasa aiki

Farfesa Osinbajo ya kuma bayyana cewa Shugaba Bashir mutum ne mai gaskiya da rikon amana. A cewar Mataimakin Shugaban kasar gyara su ka zo yi wanda ba aiki bane mai sauki ko kadan kuma a ta bakin sa yanzu haka ana aikin gyara kasar.

Osinbajo yace Gwamnatin APC na kokarin canzawa motar Najeriya inji ne wanda yace an yi raga-raga da motar a baya kuma ba za ta iya cigaba da tafiya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel