Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa 'Yan kwallon Najeriya

Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa 'Yan kwallon Najeriya

- Shugaba Buhari ya yabawa kokarin 'Yan wasan Najeriya

- Kungiyar Super Eagles ta samu zuwa Gasar World Cup

- Shugaban yace 'Yan wasan sun ba Kasar kyautar musamman

Shugaban Kasa Buhari yayi magana game da 'Yan wasan Super Eagles da su ka doke Kasar Zimbabwe jiya da yamma.

Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa 'Yan kwallon Najeriya

Shugaban kasa ya yabawa 'Yan wasan Super Eagles

Shugaba Buhari yayi magana game da nasarar da Super Eagles ta samu zuwa Gasar cin kofin Duniya da za ayi a Kasar Rasha shekara mai zuwa inda yace 'Yan wasan sun nuna bajinta da kokarin gaske.

KU KARANTA: Najeriya za ta je Gasar kofin Duniya

A cewar Shugaban kasar 'Yan kwallon sun ba kasar Najeriya kyautar musamman ne na samun 'yancin kai a wannan watan da wannan nasara. Shugaban kasa Buhari ya kuma yabawa irin gudumuwar da Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta ke yi wa tawagar 'Yan wasan na Najeriya.

Tsohon Shugaban kasa Jonathan Goodluck da Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da irin su Bukola Saraki sun yabawa 'Yan wasan. Dan wasan Arsenal Alex Iwobi ne dai ya zura kwallon daga shigowan sa wasan a raga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel