Osinbajo ya bayyana dalilin da yasa yan Najeriya ba sa iya rayuwa sai da cin hanci da rashawa

Osinbajo ya bayyana dalilin da yasa yan Najeriya ba sa iya rayuwa sai da cin hanci da rashawa

- Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sa cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a Najeriya

- Mataimakin shugaban kasa ya nuna takaici akan yadda yan Najeriya suke daukan masu cin hanci da rashawa da muhimmanci

- Cin hanci da rasahwa ya sa yan Najeriya cikin mawuyacin hali da talauci inji Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbanjo, yayi tsokaci akan yadda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a kasar, ya ce yan Najeriya ba sa iya rayuwa sai da cin hanci da rashawa.

Osinbanjo ya bayyana haka ne a wata taro da ya halarta a ranar Asabar a jihar Legas.

Mataimakin shugaban kasa ya nuna takaici akan yadda masu cin hanci da rashawa suke cin Karen su ba babbaka a kasar.

Osinbajo ya bayyana dalilin da yasa yan Najeriya ba sa iya rayuwa sai da cin hanci da rashawa

Osinbajo ya bayyana dalilin da yasa yan Najeriya ba sa iya rayuwa sai da cin hanci da rashawa

Yace “ta dalilin cin hanci da rashawa yan Najeriya suke fuskantar tsananin rayuwa da talauci a yanzu.

KU KARANTA : Yansanda sun kashe wani mutum da ake zargin sa da garkuwa da mutane a Cross Rivas

“Kuma abun takaici game da wannan al’amari shine, yan Najeriya sun fi daukan masu cin hanci da rashawa da muhimmanci.

“Da wannan mumunar hali babu yadda zamu iya gasa da kasashen da suka cigaba a duniya.

“Muna da ikon kawo karshen hanci da rashawa a kasar mu idan mun, saboda haka dole ne mu canza halayen mu, da nuna kyama ga wadanda suka yi arziki ta dalilin cin hanci da rashawa a kasar nan,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel