Kasancewa a harkokin siyasa ya kai ni ga talauci – Inji Obi

Kasancewa a harkokin siyasa ya kai ni ga talauci – Inji Obi

- Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce siyasa a Najeriya na iya talauta mutum

- Ifeanyi Ubah ya zargi Obi cedwa ya bukaci naira biliyan 7 daga gwamna Willie Obiano

- Obi ya ce kasancewa cikin harkokin siyasar ya talauta shi

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa shiga harkokin siyasa ya talauta shi a fanin kudi.

Obi ya bayyana hakan ne a mayar da martani a kan zargin da Ifeanyi Ubah ya yi masa, wanda ya yi ikirarin cewa Obi ya bukaci naira biliyan 7 daga gwamna Willie Obiano.

A cikin hirarsa da majiyar NAIJ.com, tsohon gwamna ya ce: " Za ku iya gane da kanku cewa ba suna ne kawai. Ni Krista ne kuma bai kamata na yi rantsuwa ba, amma zan iya sanya hannuna a kan kowane nau'i na rantsuwar da aka yi kuma na ce ban taba tattauna da kowa ba a kan biya wani adadin kudi. Ban taɓa yin haka ba kuma ba zan taba yin haka ba".

Kasancewa a harkokin siyasa ya kai ni ga talauci – Inji Obi

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi

"A wannan yanayin na rayuwata, ba zan iya goyi bayan kowa ba don amfanin kaina ko wani burin siyasa. Na riga na wuce wannan matsayi kuma yin haka a gare ni rashin godiya ga Allah ne. Ban shiga cikin siyasa da talauci ba”.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya sun cire rai da mulkin APC

“Kasancewa cikin harkokin siyasar ma ya sa ni talauci, amma ban yi nadama yin haka ba saboda abin da Allah ya riga ya kaddara ne”, inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel