Bincike: Shin cin ganda na da wata fa'ida ga lafiyar masu cin ta, ko kuwa mayata ce ta dan-baki

Bincike: Shin cin ganda na da wata fa'ida ga lafiyar masu cin ta, ko kuwa mayata ce ta dan-baki

- Pomo/Ganda dai ana saka wa a miya, musamman miyoyin ganye ko yaji

- Ana cin ganda sosai a kudu, fiye da a arewa, amma a hankali, arewa ma ta koya

- Ganda dai ba nama bace, ba kuma ta bata amfanin da nama ke bayarwa

A abinci irin na Afirka, na bakaken fata, ana yawan cin karo da fatar dabbar da aka saka a miya da sunan karin nama, sai dai, naman ba dukka ne nama ba, a'a, wasu lokutan, ganda ce kawai, fatar dabbar da ba lalle ta karo dadin ko armashin asalin amfanin abincin ba.

Bincike: Shin cin ganda na da wata fa'ida ga lafiyar masu cin ta, ko kuwa mayata ce ta dan-baki

Bincike: Shin cin ganda na da wata fa'ida ga lafiyar masu cin ta, ko kuwa mayata ce ta dan-baki

Ganda dai akwai cika ido, kuma bata da wani dadi nata na kanta, babu kuma wani amfani na bitamin a jikinta, kawai dai fata ce cike da mai wadda tafi amfani idan da an sarrafa ta zuwa kayan sayarwa, kamar darduma, takalma, ko gam domin manne katako.

Amma dan-baki ba ruwansa, shi dai duk wani abu daga jikin dabba sai ya cinye, ko da kuwa qaho ne ko kofato, baya bari. Kai har marena, kai da kafa, kwakwalwa da hanji, duk cinye wa yake. A wasu lokutan ma jinin ba'a zubarwa, sai a daskaras dashi a siyar a matsayin hanta.

DUBA WANNAN: An jibge jami'an tsaro a kamfanin mai na NNPC, tun bayan zargin sata

Komo dai, ko bomo, a wasu kasashen, abun amfani ne ga masana'antu masu yin kayan mata kamar jaka, da ababen kwalliya, da dardumai da shimfidu. Ana kuma yin gum da iya, saboda kayan danko da take dauke da su, a kuma aiko mana mu siya da tsada.

Amma mu a nan, sai mu kama mu jiqa, mu yanyanka mu saka magi da gishiri, mu cinye kamar dai munci farfesu, mu lashe baki wai munci dadi.

Duk amfanin da ganda dai zata bamu, sauran abinci zai bamu, kuma duk da babu wata rubutacciyar illa da gandar ke bayar wa, wasu al'adun na mana kallon mayatar mu tayi yawa, da rashin wayon iya neman kudi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel