Hukumar kwastam ta kwace wasu kwantena cike da shinkafa na waje

Hukumar kwastam ta kwace wasu kwantena cike da shinkafa na waje

- Hukumar kwastam shiyar Fatakwal ta ce ta kwace wasu kwantena cike da shinkafa na waje

- Shugaban hukumar ya bayyana cewa hukumar ta gano kayan ne saboda wata dabara na bincike da suka fara kwanan nan

- Hukumar ta koka a kan rashin kayan aiki na dubawa don gano kayan haɓaka

Hukumar kwastam na Najeriya shiyar Fatakwal ta kwace wasu manyan kwantena 3 da ke dauke da daruruwan jakar shinkafa na waje, wanda wani mai sayarwa ya yi ƙarya.

Babban kwamandan hukumar, Abubakar Bashir, ya bayyana cewa hukumar ta gano kayan ne saboda wata sabuwar shiri da hukumar ta fitar na fara aikin binciken kayayyakin da ake shigowa dari bisa dari na kowane kwantena da ke shiga cikin kasar ta hanyar hukumar.

Da yake nuna kayayyakin da aka kwace ga 'yan jarida, Bashir ya tuna cewa hukumar a karkashin jagorancinsa ta kwace kimani 23 wanda nauyin kudin sun kai miliyan 446.3 da miliyan 23.6 a kan kwantena 3 da ke dauke da shinkafa.

Hukumar kwastam ta kwace wasu kwantena cike da shinkafa na waje

Ofishin hukumar kwastam

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Bashir ya bayyana cewa mai shigowa ya bayyana cewa kwantena na dauke da kayan aiki na sutura, amma a lokacin da jami’an tsaro suka yi bincike nan aka gano cewa shinkafa ne cikin kwantena.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa 360,000 aiki kwanan nan

Shugaban kwastan shiyar Fatakwal ya koka a kan rashin kayan aiki na dubawa don gano kayan haɓaka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel