Sarkin Saudiyya yayi kaca-kaca da kasar Iran dangane da gabas ta tsakiya

Sarkin Saudiyya yayi kaca-kaca da kasar Iran dangane da gabas ta tsakiya

Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul Aziz yayiwa manufofin kasar Iran daukar karan mahaukaciya a yayin wata ziyara aiki da ya ka kasar Rasha a karo na farko a tarihin duniya da a satin da ya gabata.

A cewar Sarki Salman, dole ne fa sai kasar Iran ta fita daga harkokin takwarorin ta na kasashen gabas ta tsakiya saboda acewar sa hakan na kawo tsaiko ga kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

Sarkin Saudiyya yayi kaca-kaca da kasar Iran dangane da gabas ta tsakiya

Sarkin Saudiyya yayi kaca-kaca da kasar Iran dangane da gabas ta tsakiya

KU KARANTA: Koriya ta Arewa zata kaiwa Amurka hari

NAIJ.com dai ta samu cewa yanzu haka kasashen na Iran da Saudi Arabiya na gabza fada a kaikace ta hanyar goyon bayan bangarori a kasashen da masa ga maciji da juna.

Haka ma dai kasar ta Rasha a karkashin jagorancin shugaba Vladimir Putin na a matsayin babbar kasar da ke kawance da kasashen yan shi'a irin su Iran da Siriya duk dai a gabas-ta-tsakiyar.

Daga nan ne kuma sai Sarki Salman din na kasar Saudiyya ya nuna sha'awar sa ta sayan babban makami mai linzami samfurin S-400 daga kasar ta Rasha domin karin tsaron su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel