Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa 360,000 aiki kwanan nan

Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa 360,000 aiki kwanan nan

Gwamnan babban bankin Najeriya Mista Godwin Emefile ya bayyana yadda suka tsara wa gwamnatin shugaba Buhari hanyoyi daban daban da za su samar wa matasa akalla 360,000 ayyukan yi a fadin kasar nan.

Mista Emefile yayi wannan furucin ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin da ta hada kafa a karkashin shirin habaka harkar noma na Accelerated Agricultural Development Scheme (AADS) a turance.

Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa 360,000 aiki kwanan nan

Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa 360,000 aiki kwanan nan

KU KARANTA: Yan Najeriya sun fidda rai daga Gwamnatin APC

NAIJ.com ta samu dai cewa Gwamnan babban bankin ya shaidawa majiyar ta mu cewa a a cikin shirin, matasan da suke a tsakanin shekaru na 18 zuwa na 35 sune za su ci gajiyar shirin na gwamnatin tarayya.

A karkashin shirin, shugaban babban bankin Najeriyar ya bayyana cewa matasa dubu goma-goma ne za su anfana da shirin.

Shima a nashi bangaren, ministan harkokin noma Cif Audu Ogbeh cewa yayi za su bada taimako sosai domin ganin shirin ya samu nasara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel