An jibge jami'an tsaro a kamfanin mai na NNPC, watakil domin barakar dake tsakanin shugabbanni

An jibge jami'an tsaro a kamfanin mai na NNPC, watakil domin barakar dake tsakanin shugabbanni

Abu kamar wasa, yadda ake zargin jam'iyyar PDP da satar biliyoyin kudi, sai gashi jam'iyyar malaman chanji itama alwalarta ta karye, ana tsaka da sallah. Zarge-zargen sata sai karuwa yake tsakanin masu mulki. Talaka kuwa na cike da dukkan jam'iyyun.

An jibge jami'an tsaro a kamfanin mai na NNPC, watakil domin barakar dake tsakanin shugabbanni

An jibge jami'an tsaro a kamfanin mai na NNPC, watakil domin barakar dake tsakanin shugabbanni

Rahotanni daga babban birnin tarayya na Abuja, na cewa an ga karin jami'an tsaro an jibge su a kewayen CBD na Abujar, unguwar dda NNPC ke da zama. Central Business District dai shine layin da manyan ofisoshin gwamnati ke kai har zuwa fadar mulki.

Jami'an tsaron sun kuma karu a ofishin kamfanin mai na NNPC, inda a nan ne Najeriya ke samun kusan dukkan kudaden shigarta, ka iya cewa nan ce lakkar rayuwar tattalin arzikin kasa baki daya.

DUBA WANNAN: Babachir da Baru na tara wa Buhari kudin kamfe ne, inji PDP

A ta bakin wani ma'aikacin tsaro a wajen dai, ya ce hakan na da nasaba da badakalar da aka ji tana bullo wa tsakanin shuwagabannin kamfanin bangaren ministiri da kuma NNPC, Ibe Kachiku, wanda tsohon shugaban NNPC din ne, da kuma Maikanti Baru, shugaba na yanzu.

Kachiku dai ya rubutawa shugaba Buhari takarda ne yana tonon silili kan wai an wawure dala biliyan 25 a karkashin shugaban kamfanin Baru.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel