Najeriya ta shiga sahun kasashen da zasu buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Rasha 2018

Najeriya ta shiga sahun kasashen da zasu buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Rasha 2018

- Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta fito gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

- Wannan dai shine karo na 6 da kasar Najeriya zata buga gasar

- Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya shekara mai zuwa wato 2018 a kasar Rasha

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta fito gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a buga a kasar Rasha a shekarar 2018 mai zuwa bayan data lallasa kungiyar kwallon kafa ta Chipololo dake kasar Zambia a wasan zagayen karshe na fitar da kasashen Afrika.

Najeriya ta shiga sahun kasashen da zasu buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Rasha 2018

Najeriya ta shiga sahun kasashen da zasu buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Rasha 2018

Wannan dai shine karo na 6 da kasar Najeriya zata buga gasar wasan cin kofin kwallon kafa ta duniya.

DUBA WANNAN: Dalibin jami'a ya rasa ran sa bayan tunkarar 'yan fashi da makami

Dan wasan Najeriya, Alex Iwobi, dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake Ingila ne ya jefawa Najeriya kwallo a ragar Zambiya a daidai minti na 77 cikin wasan kuma a haka wasan ya kare.

Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya shekara mai zuwa, wato 2018, a kasar Rasha.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel