Kamfanin wutar lantarkin Inugu ya sha alwashin kamo masu satar layi

Kamfanin wutar lantarkin Inugu ya sha alwashin kamo masu satar layi

- Sun hada sabon kwamiti na bi gida-gida

- Sun samar da layin wayar hura usur

- Tarar duk wanda aka kama ta fara daga N50,000 zuwa N450,000

Kamfanin wutar lantarki na Inugu (EEDC) ya ce daga yau zai fara buga sunayen mutanen da kamfanonin da suka kama suna satar layin wuta.

Mai magana da yawun EEDC ne, Mista Emeka Eze, ya fadi haka a ranar Asabar, in da ya ce lokaci yayi da ya kamata a magance masalar masu satar layin wuta don kullum karuwa suke yi.

Kamfanin wutar lantarkin Inugu ya sha alwashin kamo masu satar layi

Kamfanin wutar lantarkin Inugu ya sha alwashin kamo masu satar layi

Ya ce baiyana sunayen zai biyo baya ne bayan sun kai su ga hukuma don a hukunta su, sannan a sa su biya bashin wutar da suka sata, da kuma tara.

"Don tafiyar da wannan, mun kaddamar da sabon kwamitin da zai na bi gida-gida don gano barayin wuta. Abin takaici shine su barayin wutar sun fi kowa shan wuta saboda kayan da suke sawa a gidajen su. Wannan babbar matsala ce; shi ya sa duk wanda muka kama baza mu yi musu mutunci ba. Sun dauka hakkin su ne suyi amfani da wutar lantarki ba sai sun biya ba. Suna cikin manyan abin da ke kawo matsalar wuta a Najeriya baki daya."

Ya gama da cewa duk wanda ka gani yana satar wuta, to sun bude sabon layin hura usur (084 700 110) don a kai musu kara.

DUBA WANNAN: Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba (DVC)

Barayin wutar lantarki suna kawo wa EEDC asarar kaso 43 daga cikin kudin da ya kamata su samu duk wata.

Hukumar wutar lantarki ta kasa kwanan nan ta sa tarar N50,000 zuwa N450,000 ga duk wanda aka kama ya yi satar layi. Sunan ganin wannan zai sa mutane su kuka daga wannan aiki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel