Dalibin jami'a ya rasa ran sa bayan tunkarar 'yan fashi da makami

Dalibin jami'a ya rasa ran sa bayan tunkarar 'yan fashi da makami

Hukumar 'yan sanda a jihar Ebonyi ta sanar ta bakin mai magana da yawun hukumar, Loveth Odah, da mutuwar wani dalibin jami'ar jihar Ebonyi mai suna Chinedu Linus bayan da ya tunkari 'yan fashi.

'Yan fashin sun kashe Linus ne ranar juma'a bayan sun tsallaka gidan dalibin don yi masa fashi. Majiyar mu ta bayyana mana cewar, 'yan fashin sun haura gidan da dalibin yake misalin karfe 1:30 na dare shi kuma yayi kokarin kare kansa ta hanyar daukar wani karfe. Makwabtan dalibin sun ce sun ji hayaniya a gidan kafin daga bisani suji karar tashin bindiga. Marigayin na zaune a wani gida dake makwabtakar dakin kwanan dalibai na jami'ar da yake karatu.

Dalibin jami'a ya rasa ran sa bayan tunkarar 'yan fashi da makami

Dalibin jami'a ya rasa ran sa bayan tunkarar 'yan fashi da makami

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewar sun samu labarin zuwan 'yan fashin kuma sun baza jam'ian su domin zuwa inda 'yan fashin suke amma saboda rashin kyan hanyar zuwa wurin basu sami damar cimma 'yan fashin ba.

DUBA WANNAN: Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba

Hukumar 'yan sandan tayi kira da hukumar makarantar data kewaye tare da gyara hanyar zuwa dakin kwanan daliban. Sannan sunyi kira ga daliban da su guji tunkarar 'yan fashi da makami ko 'yan bindiga.

Tuni dai aka ajiye gawar dalibi, Linus, a dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa dake Abakaliki, Babban birnin jihar ta Ebonyi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel