Kasar Sifen zata rabe gida 2 a ranar 9 ga watan Oktoba

Kasar Sifen zata rabe gida 2 a ranar 9 ga watan Oktoba

Yankin nan na Catalonia dake a kasar Spain ya ayyana ranar Litinin 9 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za su balle su kafa kasar su mai cin gashin kanta biyo bayan zaben raba gardama da suka gudanar satin da ya gabata.

Takaddamar dai da yanzu ake yi kuma ita ce ta yadda ita uwar kasar ta Sifen ta yi fatali da sakamakon zaben raba gardamar ta kuma nuna kin amincewa da kudurin su ka ballewa daga kasar.

Kasar Sifen zata rabe gida 2 a ranar 9 ga watan Oktoba

Kasar Sifen zata rabe gida 2 a ranar 9 ga watan Oktoba

KU KARANTA: Hukumar zabe ta dakatar da zaben kananan hukumomin Kaduna

NAIJ.com ta samu dai cewa u kuma a nasu bangaren jagororin shirin ballewar na kasar Cataloniyar irin su Mireia Boya sun bayyana cewa a ranar ta Litinin mai kamawa za su yi zama na musamman a majalisar kasar su.

Kasar Sifen dai ta dawo bisa tafarkin Demokradiyya ne tun bayan mutuwar shugaban kasar na mulkin soja Francisco Franco a shekara ta 1975 inda kuma daga lokacin yan yankin Catalan suke kukan mai da su saniyar ware.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel