An gano wasu manyan gidajen alfarma mallakar 'yan Najeriya a kasar Ingila

An gano wasu manyan gidajen alfarma mallakar 'yan Najeriya a kasar Ingila

Rahotannin da muke samu daga majiyoyi da dama sun tabbatar mana da cewa wata kungiya mai zaman kanta da ba ta gwamnati ba wadda ke yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Birtaniya ta bankado wasu gidajen alfarma na milyoyin kudade mallakar wasu manyan yan Najeriya.

Kungiyar dai mai suna Clampk a turance a kwanan baya ta gudanar da wani muhimmin binciken rangadi na musamman inda ta rika nuna bidiyon wadannan gidaje a cikin rahoton su da suka kammala.

An gano wasu manyan gidajen alfarma mallakar 'yan Najeriya a kasar Ingila

An gano wasu manyan gidajen alfarma mallakar 'yan Najeriya a kasar Ingila

KU KARANTA: Kalli wani jirgi da matashi daga Yobe ya kera

NAIJ.com ta samu dai cewa haka zalika sakamakon wannan binciken nasu ya tabbatar da cewa cikin masu wadannan gidajen hadda yan majalisaun tarayya, wani tsohon Shugaban kasar a mulkin soja da ma kuma wani tsohon hafsan Sojan Najeriya wanda ke cikin gwamnatin APC ta Buhari a halin yanzu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaba Muhammadu Buhari a kwanan baya ya bukaci wata yarjejeniyar hadin gwuiwa da gwamnatin kasar Birtaniya inda yake so ya fara kwato dukiyar kasa da aka kwace aka kai kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel