Da dumin sa: Tankokin mai sun kama da wuta a kusa da Abuja

Da dumin sa: Tankokin mai sun kama da wuta a kusa da Abuja

Wani labari maras dadin ji da ya same mu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa yanzu haka wata mummunar gobara ta kama a garin Tafa dake a kusa da Abuja sakamakon wasu manyan motoci tankokin mai da suka kama da wuta.

Mummunar gobarar kamar yadda muka samu ta katse zirga zirga a kan babbar hanyar ta Abuja zuwa Kaduna a garin na Tafa inda manyan motoci ke tsayawa.

Da dumin sa: Tankokin mai sun kama da wuta a kusa da Abuja

Da dumin sa: Tankokin mai sun kama da wuta a kusa da Abuja

KU KARANTA: Duk masu kashe mutane da sunan jihadi wuta za su - Sultan

NAIJ.com dai ta samu cewa motocin tanka ne da ke dauke da mai da dama suka kone a garin na Tafa. Dama dai garin na Tafa ya yi kaurin suna wurin taruwar manyan motocin tankokin man fetur.

Haka ma dai kuma mun samu cewa yanzu akan aukuwar wannan gobarar ta sa dole matafiya sun sake hanya inda suka fara bin hanyar Jere domin zuwa garin na Abuja.

Wasu wadanda suka ganewa idon su yadda al'amarin ya auku sun shaidawa majiyar mu cewar akalla tankokin mai uku ne suka kone a gobarar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel