Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba (DVC)

Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba (DVC)

- Oke ya lashe zabe da kuri'u 77, mai bi masa kuma yana da 39

- Shi ne tsohon Din na Fakwaltin Kimiyya

- Zai rike mukamin na shekara biyu

A zaben da aka yi jiya na takarar kujerar mataimakin shugaban jami’ar Legas (LASU), Farfesa Oyedamola Oke, na sashen (Fakwaltin) Kimiyya, ya samu nasarar samun kujerar.

Mai magana da yawun bakin jami’ar ne, Mista Adekoya Martins, ya baiyana wa manema labarai haka.

Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba (DVC)

Jami'ar Legas ta nada Oke a matsayin matamakin shugaba (DVC)

Ya ce Oke ya lashe zaben ne da kuri’u 77, inda abokin takarar sa, Farfesa Banji Fajonyomi, kuma yana da kuri’u 39.

Shugaban jami’ar ya baiyana farin cikin sa da Oke ya samu nasara, kuma ya ce wannan zaben da aka yi ba magudi a cikin sa.

“Ko da aka fadi sakamakon zaben, halin da ‘yan takar suka nuna ya nuna cewa suna da kamala cikakkiya. Kuma ina kyautata zaton zasu hada kai don samar da ci gaban jami’ar mu.”

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno ya yanke jiki ya fadi matacce a masaukin sa

Oke ya gaji kujerar ne daga hannun Farfesa Fidelis Njokanma na sashen Likitanci, kuma zai rike kujerar tsawon shekaru biyu kafin a sake wani zaben.

Oke shine tsohon shugaba sashen Kimiyya (Dean Faculty of Science), sannan kuma a yanzu haka shine me kula da diban sababbin dalibai.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel