Alakar tayar da kayar baya na gwamnatocin shugaba Buhari da Jonathan - Gwamna badaru

Alakar tayar da kayar baya na gwamnatocin shugaba Buhari da Jonathan - Gwamna badaru

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Abubakar Muhammad Badaru, ya bayyana alakar dake tsakanin tayar da kayar baya na karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da na tsohuwar gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan.

Yayin da gwamnan yake alakanta gwamnatocin biyu, ya kuma bayyana cewa tayar da kayar baya ba laifi ba ne matukar an kare dukkan wani hakki na doka wajen tayarwar.

Alakar tayar da kayar baya na gwamnatocin shugaba Buhari da Jonathan - Gwamna badaru

Alakar tayar da kayar baya na gwamnatocin shugaba Buhari da Jonathan - Gwamna badaru

A cewarsa, "tambaya a nan ita ce, shin wannan tayar da kayar bayan yana da wani tasiri ko manufa? Kuma me yasa sai yanzu? Ina masu tayar da kayar bayan suka shiga kafin zuwan wannan gwamnatin?"

KARANTA KUMA: Kaico: Yadda miyagun ƙwayoyi ke barazana ga makomar Arewacin Najeriya

"Ko kuma gwamnatin baya ta danne tare da gallazawa hakkoki shi hana su fitowa su bayyana ra'ayoyinsu? Wadansu daga cikin masu tayar da kayar bayan a yanzu 'yan siyasa ne na gidi, wasusunsu sun tsaya takara sun fadi. Ni da kaina na san wadanda suke neman a tsawaita lokacin akan kujerun shugabanci."

"Ni a fahimtar da na yi, duk da rashin jin dadin da suke yiwa na gwamnatin, hakan bai kamata ya sanya su tayar da kayar baya ba, sai su fito domin a cigaba da jan akalar shugabancin kasar nan tare da su. Su yi amfani da mukamansu na siyasa kamar yadda dokar da tsarin kasa ya tanadar".

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel