Abuja: Allah ya ba wa 'yan Najeriya haƙuri don jure wa gwamnatin mu – Inji Buhari

Abuja: Allah ya ba wa 'yan Najeriya haƙuri don jure wa gwamnatin mu – Inji Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Allah ya ba 'yan Najeriya haƙuri da dauriya don jurewa gwamnatinsa

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa na iya kokarin ta wajen magance kalubalen da ta gaji daga magabatansa

- Shugaba Buhari ya lura cewa yanzu ne gwamnatinsa ta fara aiki gadan-gadan

Shugaban kasar Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba ya yi fatan aiheri cewa "Allah a cikin rahamarsa” zai ba 'yan Najeriya haƙuri da dauriya don jurewa gwamnatinsa.

Da yake jawabi a fadar shugaban kasa a birnin Abuja, shugaba Buhari ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta na iya kokarin ta wajen magance kalubalen da ta gaji daga magabatansa.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, shugaba Buhari ya lura cewa yanzu ne gwamnatinsa ta fara aiki gadan-gadan.

Abuja: Allah ya ba wa 'yan Najeriya haƙuri don jure wa gwamnatin mu – Inji Buhari

Shugaban kasar Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya ce, "Na sha yin wannan zance, kuma ba zan damu na sake faɗa muku yanzu ba saboda wasu daga cikinku ba su da lokaci don sauraron rediyo ko kallon talabijin kamar yadda sauran mutane ke yi".

KU KARANTA: Biyafara : Abun da Buhari ya fada mun game da masu fafutika – Gwamna Umahi

"Daga 1999 zuwa 2014, Najeriya ba ta taba samun wadataccen albarkatu ba tun lokacin da muka samu 'yanci, kuma Najeriya na hako ganga man fiye da miliyan 2.1 a kowace rana a kimanin dala Amurka 100 a kan kowane ganga”.

"Amma lokacin da muka karbi mulki daga gwamnatin da ta gabata farashin man ta fado zuwa dala 37 na kowane ganga, kuma a wancan lokacin mun manta cewa ya kamata mu yi ajiya saboda gobe”.

"A gaskiya Allah, yanzu muka fara aiki kuma muna fatan Allah a cikin rahamarsa zai ba al’ummar Najeriya hakuri don jurewa gwamnatin mu", inji shugaba Buhari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel