'Yan Najeriya sun cire rai da mulkin APC

'Yan Najeriya sun cire rai da mulkin APC

- Ezekiel Adaji, wani Dan Majalisar Dokoki karkashin tutar PDP ne ya fadi hakan

- Ya fadi hakan ne yayin kaddamar da kwallon kafa da ya tsarawa matarsa mazaban sa. A cewar sa hakan ita ce hanya mafi sauki da zai tallafa masu

- Ya ce canji da APC ta ke ikirari ba komai bane illa iface-iface da ba su da kai ba su da tushe

Ezekiel Adaji, wani Dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Otukpo/Ohimini a karkashin tutar PDP, ya ce 'yan Najeriya ba su da rabo a karkashin mulkin APC. Ya fadi hakan ne yana mai kafa hujja da tsanani bayan tsanani da wasu 'yan Najeriya ke fadawa.

'Yan Najeriya sun cire rai da mulkin APC

'Yan Najeriya sun cire rai da mulkin APC

Adaji ya ce canji da APC ta ke ta fadi ba komai bane illa iface-iface da ba su da kai kai ba su da tushe wanda kuma ba zai fitar da 'yan Najeriya cikin matsalolin da suke ciki ba. Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kwada APC a kasa a zaben 2019 mai zuwa.

DUBA WANNAN: Abun mamaki: Wani gari da maza ke shigar mata

Ya fadi hakan ne a wurin kaddamar da gasan kwallon kafa da ya tsara ma mazabar da yake wakilta. Ya ce yin hakan ita ce hanya mafi sauki da zai tallafawa mazabar nasa. Ya yi ikirarin ba ya yi da nufin kamfen bane.

Ya kuma jaddada cewan a matsayin sa na tsohon dan siyasan da ya dade yana wa al'umma hidima, lallai zai bunkasa gasar kwallon kafan ta hanyar tallatama abokan sa don a cigaba da gudanar da shi ko bayan kare wakilcin sa.

A cewar sa, lallai gasar kwallon kafan na da muhimmaci wurin tallafawa matasa da kuma rage faruwan barna tsakanin masu zaman banza.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel