Biyafara ba ta cikin ajandan iyan kabilar Igbo – Inji Ohanaeze

Biyafara ba ta cikin ajandan iyan kabilar Igbo – Inji Ohanaeze

- Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya bayyana cewa Biyafara ba ta cikin ajandan kungiyar

- An kaddamar da shugabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a jihar Abiya

- Nwodo ya ce ya kamata yankin kudu maso gabas su manta da zancen Biyafara

Shugaban kungiyar ‘yan kabilar Igbo Ohanaeze Ndigbo, Cif John Nnia Nwodo, a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba ya ce fafutukar kafa yankin Biyafara ba ajandan al’ummar kudu maso gabashin kasar ba ne, yana maida martanin cewa sake gyaran tsarin mulkin Najeriya na daga cikin abubuwan da kungiyar ke goyon baya.

NAIJ.com ta tattaro cewa, shugaban ya sanar da wannan a Umuahia, a cikin jawabinsa a taron kaddamar da shugabannin jihar da kuma kanannan hukumomi shiyar Abiya na kungiyar Ohanaeze Ndigbo.

Matsayin kungiyar Ohanaezw wanda Nwodo ya bayyana, ta sha bamban da na kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB), wandanda ke gwagwarmaya don kafa yankin Biyafara.

Biyafara ba ta cikin ajandan iyan kabilar Igbo – Inji Ohanaeze

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif John Nnia Nwodo

Nwodo ya ce: "Ya kamata mu manta da zancen Biyafara, amma za mu ci gaba da matsa lamba a kan sake gyaran tasarin mulkin kasar", inji shi.

KU KARANTA: Abuja: Allah ya ba wa 'yan Najeriya haƙuri don jure wa gwamnatin mu – Inji Buhari

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Fallasa: Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna

Fallasa: Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna

Fallasa: Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna
NAIJ.com
Mailfire view pixel