Dalilin da ya sa Biyafara ba zata taba gushewa ba, Inji Ikedife

Dalilin da ya sa Biyafara ba zata taba gushewa ba, Inji Ikedife

- Dozie Ikedife wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo ya fadi hakan

- Ya ce biyafara kamar wata asali ce ga wasu 'yan kudu maso Gabas don haka barin sa zai yi wuya gare su

- Ya kuma ce sai an daina wariya da nuna bambanci za'a daina samun irin wadannan hayaniyan

Dozie Ikedife wanda shine tsohon shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo ya sakankance lallai Biyafara ba zata gushe ba kuma ba za'a manta da ita ba saboda tana da matukar muhimmanci ga wasu 'yan yankin Kudu maso Gabas kuma ta zama kamar wata asali gare su.

Dalilin da ya sa Biyafara ba zata taba gushewa ba, Inji Ikedife

Dalilin da ya sa Biyafara ba zata taba gushewa ba, Inji Ikedife

A cewar sa, mutum ba zai taba barin asalin sa ba. Ya ce kamar yadda ba zai yiwu bayarbe ko bahaushe ya bar asalin sa ba, haka shi ma dan kabilar ta Igbo ba zai bar na sa ba.

DUBA WANNAN: Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

Ikedife wanda a yanzun shi ne dankon da ke rike da Kungiyar Dattawan Gabashi, ya ce tun a da yana da fahimtar cewa ta hanyar zaman lafiya da siyasa da fahimtar juna da bin doka ne kawai kabilar Igbo za su kai ga ci ma burin su.

Ya kuma ce dabi'a ce ta dan adam ya nemi gyara zama idan zaman bata yi ma shi ba. Don haka har sai an daidaita sahu an kuma daina wariya da nuna banbanci sannan za'a daina samun irin wadannan hayaniyan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel