Yansanda sun kashe wani mutum da ake zargin sa da garkuwa da mutane a Cross Rivas

Yansanda sun kashe wani mutum da ake zargin sa da garkuwa da mutane a Cross Rivas

- Yansadan jihar Cross Rivas sun ceci wata mata daga hanun ma su garkuwa da mutane

- Yannsanda sun yi amfani da lambar wayar ta suka gano inda ta ke bayan an sace ta

- Hukumar yansanda ta samu binigogi da layoyi da wayar tarho a cikin gidan da masu garkuwa da mutanen suke zama

Jam’ian yansanda jihar Cross Rivas sun kashe wani mutum da ake zargin sa da laifin garkuwa da mutane a Okonyong dake karamar hukumar Odukpani a jihar Cross Rivas.

An zargi mammacin tare da yan kungiyar sa da yinn awon gaba wata mata wanda ba a bayyana sunan ta ba.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa, daya daga cikin ma su garkuwa da mutanen ya yi amfani da wayar matar, aka kira yan uwanta dan shirya yadda za a anshi kudin da za a fanshi rauywarta da shi.

Yansanda sun kashe wani mutum da ake zargin sa da garkuwa da mutane a Cross Rivas

Yansanda sun kashe wani mutum da ake zargin sa da garkuwa da mutane a Cross Rivas

Yansanda sun gano inda masu garkuwan da mutanen suke ne ta lamabar wayar matan da aka kira yan uwanta da shi.

KU KARANTA : Matana barauniya ce, kyamaran da na boye ya nuna ta na kwana da mazaje da yawa – Magidanci ya fada wa kotu

Yansanda sun kashe wanda yayi kiran a lokacin da suka isa wajen, sauran yan kungiyar sun samu nasarar tserewa yansadar.

Yansanda sun ceto rauwar matar, kuma sun samu bindigogi, wayoyi da layoyi a cikin gidan da masu garkuwan suke zama.

Hukumar yansandar jihar ta yi alkwarin kama sauran yan kungiyan da suka gudu.

Mai magana da yawun hukmar yansadar jihar PPRO Ms Irene Ugbo ta tabbatar da aukuwan wanan lamari, kuma ta ce jam’ian su suna kan neman sauran yan kungiyar da suka gudu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel