Zabe: INEC ta dakatar da zabukan kananan hukumomi a Kaduna

Zabe: INEC ta dakatar da zabukan kananan hukumomi a Kaduna

- Hukumar INEC ta sanar da dakatar da zabukan kananan hukumomi a jihar Kaduna

- Shugaban hukumar ta sanar bayan taron gaggawa tare da kwamitin shari’a na majalisar dokokin jihar

- Hukumar ta ce jinkirin ya zama dole yayin da majalisa ba ta amince da sabon dokar da za ta jagoranci zaben ba

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC sashe na jihar Kaduna a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba ta sanar da dakatar da zaben kananan hukumomi na tsawon lokaci wanda aka shirya za a gudanaar a ranar 30 ga watan Disamba.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labarri, shugaban hukumar, Malama Saratu Dikko ta yi sanarwa bayan taron gaggawa tare da kwamitin shari’a na majalisar dokokin jihar a Kaduna.

Shugaban ta bayyana wa manema labarai bayan taron cewa an dakatar da zaben.

Zabe: INEC ta dakatar da zabukan kananan hukumomi a Kaduna

Shugaban hukumar INEC ta kasa, Mahmood Yakubu

A cewarta, jinkirin ya zama dole yayin da majalisa ba ta amince da sabon dokar da za ta jagoranci zaben ba.

KU KARANTA: Bode George na neman takarar Shugabancin PDP

"A duk lokacin da aka amince da dokar da kuma gwamna ya sanya hannu, zamu yi sabon sanarwa game da zaben", in ji ta.

Har ila yau, shugaban kwamitin majalisar, Mista Kantiok Ishaku, ya ce ba daidai ba ne ga hukumar ta sanar da ranar da za a gudanar da zabenn kananan hukumomi yayin da majalisa ba ta kammala aiki a kan dokar zaben ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel