Biyafara : Abun da Buhari ya fada mun game da masu fafutika – Gwamna Umahi

Biyafara : Abun da Buhari ya fada mun game da masu fafutika – Gwamna Umahi

- Dave Umahi ya bayyana abun da Buahri ya fada mi shi game da masu fafutika

- Shugaban kasa yayi alkawarin duba matsalolin da yanki kudu maso gabas ta ke fuskanta inji Umahi

- Umahi ya yaba da kokarin da gwamnoni suka yi wajen kawo karsehn rikicin da ya barke a kwanaki baya

Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnoni kudu maso gabas, David Umahi ya bayyana cewa shugaban kasa Muahammadu Buhari ya tabbatar mi shi da duba matsalolin da yankin su ta ke fuskanta a ganawa na musamman da suka yi a New York lokacin da suka halarci taron majalissar dinkin duniya.

A lokacin da yan jaridar Sun su kama mi shi tambaya game da al’amarin masu fafutikar neman yanci Biyafara IPOB da kuma haramta kungiyar da gwamnoni yankin kudu maso gabas su ka yi.

Biyafara : Abun da Buhari ya fada mun game da masu fafutika – Gwamna Umahi

Biyafara : Abun da Buhari ya fada mun game da masu fafutika – Gwamna Umahi

Umahi ya ce, “Ni da shugaban kasa mun gana da juna game da wannan al’amari a New York, kuma ina tabbatar da mutanen yankin kudu maso gabas da cewa shugaban kasa sai zai kawo karshen matsalolin mu.

KU KARANTA : An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano

“Za a samu zaman lafiya a Najeriya. Mun fi karfi da kima idan muna tare da juna,"inji shi.

“Kuma ina son na yi amfani da wannan dama na gode wa gwamnonin kudu maso gabas da gwamnoni Arewa akan kokarin da suka wajen kawo karshen rikicin da ta barke kwanaki baya.

“Bai dai dai ba ne mu cigaba zagin shugabanin mu da sauran kabilu. Zaman lafiya da hadin kai m kasar muke bukata a yanzu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel