Rundunar Sojin Kasa ta mayar da 'yan Boko Haram 760 hannun Gwamnatin Jihar Borno

Rundunar Sojin Kasa ta mayar da 'yan Boko Haram 760 hannun Gwamnatin Jihar Borno

- Kanal Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya gabatar a Maiduguri

- Mutanen an kama su ne yayin gudanar da aiki mai taken Lafiya Dole

- Bayan bincike da bin kwakkwafi sai aka mika su sashin kulawa na Jihar don a gyatta su

A ranar Juma'a ne Rundunar Sojin Kafa, ta baki Kanal Onyema Nwachukwu ta sanar da cewan ta mayar da mutane 760 da ake zargin 'yan Boko Haram ne zuwa hannun Gwamnatin Jihar Borno don mayar da su cikin al'umma.

Rundunar Sojin Kasa ta mayar da 'yan Boko Haram 760 hannun Gwmnatin Jihar Borno

Rundunar Sojin Kasa ta mayar da 'yan Boko Haram 760 hannun Gwmnatin Jihar Borno

Nwachukwu ya ce mutanen an kama su ne yayin gudanar aiki mai taken Lafiya Dole sai aka mika su sashin kulawa da ke Bulunkuti na Jihar domin a gyatta su.

DUBA WANNAN: Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

Nwachukwu ya kara da ce an mika su zuwa sashin kulawa don gyaran ne sakamakon barrantar da su da aka yi bayan bin kwakkwafi da bincike da aka gudanar.

Ya kuma yi kira ga mutane da su sanar da jami'an tsaro da duk wani mutum ko wata hulda ko kaikomo da ba su aminta da shi ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel