Duk masu kashe mutane da sunan Allah wuta za su - Sultan

Duk masu kashe mutane da sunan Allah wuta za su - Sultan

- Sarkin musulmai Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi Alla-wadai da masu kashe mutane da sunan Allah

- Sultan ya danganta Fulanin da ke kashe mutane a matsayin 'yan ta'adda ba manoma ba

- Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da na jihar Delta Ifeanyi Okowa sun nanata yadda bawa ilimi muhimmanci ke da amfani

Sarkin musulmai Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi Alla-wadai da masu kashe mutane da sunan Allah domin kuwa ba inda zai kai su yin hakan sai wuta.

Ya fadi hakan ne a yayin da yake gudanar da wata lakca a jami’ar garin Nsukka, yace 'duk karya ce mutane su yadda da irin wannan zancen', da kara jaddada cewa kowa yana da hakkin rayuwa, musulmi ko kafiri da wanda ma basu da addini.

Duk masu kashe mutane da sunan Allah wuta za su - Sultan

Duk masu kashe mutane da sunan Allah wuta za su - Sultan

Sultan ya bayyana cewar "addinin Islama baya goyon bayan kisan duk wanda ba musulmi ba, kuma duk mai kyakykyawar fahimtar addini ya san haka, saboda haka duk mai aikata kisa yana yana kiran "Allahu Akbar" wuta zai shiga idan ya mutu".

Sultan din ya danganta Fulanin da ke kashe mutane a matsayin 'yan ta'adda ba manoma ba. Sarkin ya yi magana yadda ya kamata a gane kowace al’ada a fadin kasa, lokaci yayi da za a ce duk wani ko wata kungiya da ke tunzura rashin kan kasa an kawar da shi

DUBA WANNAN: Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019 — PDP

Sultan ya bayyana muhimmancin ilimi a rayuwar dan adam tare da kara bayanin cewar duk kasar dake son jama'ar ta su kasance cikin farinciki, dole su rike ilimi hannu biyu.

Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da na jihar Delta Ifeanyi Okowa sun nanata a kan yadda bawa ilimi muhimmanci ke da anfani a matsayin shine jigon cigaban kowace al’umma.

Tun a farkon jawabin bude taro, shugaban jami'ar ta NSUKKA, Farfesa Benjamin Ozumba, ya bayyana cewar muhimmancin baiwa manyan baki damar yin lakca shi ne domin su yi tsokaci a kan muhimman al'amura dake damun kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel