Abun mamaki: Wani gari da maza ke shigar mata

Abun mamaki: Wani gari da maza ke shigar mata

- An gano wani gari da maza ke shigar mata

- Maza na shigar mata sau daya a shekara a wani gari mai suna Owo

- Su na yin hakan ne don karrama wata uwargijiyar su mai suna Oronsen

Akwai wani gari da maza ke shigar mata a wani bikin shekara-shekara da su ke yi mai suna Bikin Igogo don karrama wata uwargijiyar su mai suna Oronsen.

Ita dai Oronsen matar sarki na 9 a garin ne mai suna Rerengenjen. Al'ummar garin tun a wancen lokacin sun yi imani Oronsen alliya ce. Ita ce gindaya ma sarkin dokar dole duk shekara sai anyi bikin karrama ta. Sai dai kuma kar a buga ganga ko kadan a bikin.

Wani gari da maza ke shigar mata

Wani gari da maza ke shigar mata

Ta kakaba masu wanna doka ne sakamakon karya wasu dokokin ta da sauran matan sarkin suka yi. Ta yi hakan baya ga yajin har abada da ta yi ne.

DUBA WANNAN: Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

A wannan biki dai sarkin garin yana fitowa daga fadar sa cikin tsabar shiga da kwalliyar mata yana kada shantun gongi yayin da yake tafiyar kasaita, lokaci bayan lokaci kuma yana taka rawa yana rausayawa. Daukacin mazan garin suma kwalliyar matan su ke yi.

Wannan Biki na Igogo ya yi kama da bikin Gerewol na fulanin Kasar Nijar da suke gudanar wa a kusa da Agades.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel