Kaico: Yadda miyagun ƙwayoyi ke barazana ga makomar Arewacin Najeriya

Kaico: Yadda miyagun ƙwayoyi ke barazana ga makomar Arewacin Najeriya

Yankin Arewa kusan shine mafi girma a fadin Najeriya baki daya, sai dai kash wannan yanki yana fuskantar kalubale da kuma barazana ga makomar sa. Kafin wannan lokaci da muke ciki a yanzu, matsaloli mafi girma a Arewa sun hadar da talauci, rashin bin doka da kuma zama cikin duhun jahilci wanda rashin neman ilimi musamman na zamani ke janyowa.

A yau matsalar da miyagun ƙwayoyi ke jefa al'ummar Arewa musamman ma matasan wannan sashe ya zama abin kaico.

A cikin rahotanni da shafin Daily Trust ya ruwaito na kwana-kwanan nan, hukumar yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewa, yin amfani da miyagun ƙwayoyi na da alhakin kashi 99 cikin 100 na laifukan da ake aikatawa a jihar Kaduna kadai.

Kaico: Yadda miyagun ƙwayoyi ke barazana ga makomar Arewacin Najeriya

Kaico: Yadda miyagun ƙwayoyi ke barazana ga makomar Arewacin Najeriya

Da yake jawabin na sa a taron wayar da kai da karin haske akan illolin miyagun ƙwayoyi wanda kungiya mai zaman kanta ta Voice of the People ta shirya, wakilin hukumar NDLEA reshen jihar Kaduna Dokta Ibrahim Baba ya bayyana cewa, yana daga cikin manufofin hukumar su ilmantar da kuma wayar da kan matasa game da haɗarin da illolin amfani da miyagun ƙwayoyi.

KARANTA KUMA: Jirgin ruwa ya sake dilmiyewa da mutane 11 a jihar Kebbi

Dokta Baba ya ce, "ba wai kawai daidai ba ne kamawa da kuma gurfanar da masu aikata laifin da yake da alaka da miyagun ƙwayoyi, amma baiwa yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi manufa wajen zagayen da muke domin fadakarwa da kuma wayar da kai da zai tallafa wajen samar da hanyoyi na yin raigakafi ga rukunin jama'ar da ke kawo barazana don su kasance sun kawar da miyagun ƙwayoyi da dukkan wani abu dake alaka da su".

"Abin da ya fi ci ma ni tuwo a kwarya shine, mafi yawan masu amfani da kayan maye a Arewa yara ne da matasa. Wasu daga cikin su sun yi rashin dace na yada makarantun almajiranta da suke yi. Sau da dama an yi ta fadakarwa kan yadda makarantun almajiranta ke kawo zagon kasa a yankunan Arewa, yayim da wasu daga cikin su suke da tsari na daidai baya ga su ke da sabanin haka".

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel