Sarki Salman na Saudiyya ya gana da Shugaba Vladimir Putin; ya ci alwashin kawo karshen gallazawa Falasdinawa

Sarki Salman na Saudiyya ya gana da Shugaba Vladimir Putin; ya ci alwashin kawo karshen gallazawa Falasdinawa

- Sarkin kasar Saudiyya ya ziyarci shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a fadar sa dake birnin Mosko

- Ya zargi kasar Iran da hura wutar rikicin kasashen musulmi na gabas ta tsakiya

- Sarki Salman ya nuna alhinin sa game da matsanancin hali da falasdinawa suka kwashe shekaru suna fuskanta daga yahudawan Isra'ila

Sarkin kasar Saudiyya, Salman Bin Abdul Aziz, ya ziyarci shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a fadar sa dake birnin Mosko domin tattauna batun zaman lafiyar gabas ta tsakiya da kuma nemawa mutanen Faladin saukin gallazawar da suke sha a hannun yahudawa.

Sarki Sulaiman ya gana da Shugaba Vladimir Putin a kan Falasdinawa

Sarki Sulaiman ya kaiwa Shugaban kasar Rasha ziyara

A yayin wannan ziyara, Sarki Salman, ya zargi kasar Iran da hura wutar rikicin kasashen musulmi na gabas ta tsakiya ta hanyar yin shishshigi da katsalandan a harkokin dake da alaka da gabas ta tsakiya.

DUBA WANNAN: Mabiya Shi'a sun bukaci shugaba Buhari ya bayyana dalilinsa na kin sakin Zakzaky

Hakazalika Sarki Salman ya nuna alhinin sa game da matsanancin hali da falasdinawa suka kwashe shekaru suna fuskanta daga yahudawan Isra'ila.

"Zamu kawo karshen gallazawar da Falasdinawa ke sha ta hanyar amfani da karfin kasashen larabawa, da kuma samar da dokokin zaman lafiya na kasa da kasa, a yunkurin tabbatar da dawwamanman zaman lafiya da kwanciyar hankali a Falasdinu, dama yankin gabas ta tsakiya baki daya".

A karshe sarki Salman yayi jan hankali game da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya a kasar Iraqi tare da kira da musulmi su zama tsintiya madauri daya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel