Siyasa: Buhari ya bayyana gwamnonin da suke bai wa gwamnatinsa hadin kai

Siyasa: Buhari ya bayyana gwamnonin da suke bai wa gwamnatinsa hadin kai

- Shugaba Buhari ya bayyana gwamnonin da suke bai wa gwamnatin APC hadin kai tun farkon wannan mulki

- Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP su 2 suna daga cikin wadanda shugaba Buhari ya jinjjinawa

- Shugaban ya ce gwamnonin sun yi wa takwarorinsu zarra ne wurin bunkasa aikin noma da inganta rayuwar al'umma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnoni su 13 daga cikin gwamnonin 36 da ke bai wa gwamnati mai mulki ta APC hadin kai wurin bunkasa tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al'umma.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnonin ne a jawabinsa ga al’ummar kasar a lokacin bikin cika shekaru 57 da samun ‘yancin daga kasar Birtaniya.

Kamar yadda jaridar Alfijir ta ruwaito cewa 2 daga cikin gwamnonin sun kasance ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne yayinda sauran 11 'yan jam'iyyar mai mulki ta APC.

Siyasa: Buhari ya bayyana gwamnonin da suke bai wa gwamnatinsa hadin kai

Shugaba kasa Muhammadu Buhari

Wadannan gwamnonin da suka samu amincewar shugaba Muhammdu Buhari sun hada da Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi (APC), Akinwunmi Ambode na Legas (APC) , David Umahi na Ebonyi (PDP) da Badaru Abubakar na Jigawa (APC) , wadannan gwamnoni ne shugaban Buhari ya ce sun yi fice wurin bunkasa noman shinkafa da samar da takin zamani ga manoma.

Sauran gwamnoni 9 da shugaban kasar ya jinjinawa, ya ce sun yi wa takwarorinsu zarra ne wurin bunkasa noman kwakwar man ja, roba, kashu, rogo, dankali da sauran tsirran da ake nomawa don kasuwanci.

KU KARANTA: Zaben 2019: Shekarau ya sha alwashin fafatawa da shugaba Buhari

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, wadannan gwamnoni sun hada da Rotimi Akeredolu na Ondo (APC), Godwin Obaseki na Edo (APC), Rochas Okorocha na Imo (APC), Benedict Ayade na Cross River (PDP), Samuel Ortom na Binuwai, Ibikunle Amosun na Ogun (APC), Nasir el-Rufa’i na Kaduna (APC) da kuma Simon Lalong na Filato (APC).

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel