Evans ya ci gaba da yadda yake so a gidan kurkuku

Evans ya ci gaba da yadda yake so a gidan kurkuku

Abun dai kamar wasan kwaikwayo bisa ga yadda jaridar Vanguard ta zayyano, sakamakon yadda ake kwashewa da shahararren mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, wanda yake tsare a gidan kurkuku na kiri-kiri tare da hukumar 'yan sanda.

Hukumar 'yan sanda ta yi kokarin kwace manyan motocin na Evans, inda shi kuwa yana daga zaune a gidan kaso yake bayar da umarnin yadda za a yi domin hana hukumar karbar wannan motoci na shi.

Evans ya ci gaba da yadda yake so a gidan kurkuku

Evans ya ci gaba da yadda yake so a gidan kurkuku

Evans ya baiwa surukin shi Mista Okwuchukwu Obi tare da hadiminsa Mista Chidozie Obiora umarnin akan yin dabarar hana jami'an na 'yan sanda karbar wannan motoci wanda suka aiwatar kuma hakan ya yi sanadiyar hana hukumar karbar dukiyar ta sa.

KARANTA KUMA: An kama shugaban matan jam'iyyar APC cikin almundahanar N1.5m

Naij.com ta fahimci cewa, Evans ya yi wannan dabarar ne domin hakan zai ba shi damar sayar da wannan motoci domin ya samu kudin biyan belinsa daga dauri.

Wannan abu ya faru kwana guda bayan jaridar Vanguard ta buga wani rahoto akan daular dukiya da Evans ya ke da ita, inda Evans ya sanya makarrabansa suka cire injina masu sanya mota tashi, wanda bayan 'yan sanda sun yi iya kacin bakin kokarinsu sai dai suka hakura suka bar su.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel