Sojin Kasa sun yi wata gagarumar nasara a jihar Imo

Sojin Kasa sun yi wata gagarumar nasara a jihar Imo

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne rundunar sojin kasa na Najeriya ta bayyana cewa, ta yi nasarar cafke wasu 'yan kungiyar asiri, masu tayar da zaune tsaye da kuma wani mai fataucin kayan maye sakamakon gudanarwar su da suke ta "Rawar Damatsiri ta Biyu" (Python Dance II).

Mataimakin mai hurda da jama'a kuma kakakin bataliyya ta 82 Kanal Sagir Musa, ya bayyana hakan inda ya tabbatar da cafkar wannan miyagu da rundunar ta yi kuma har sun mika su ga hukumar 'yan sanda domin ci gaba da bincikar su.

Naij.com ta fahimci cewa, wannan gudanarwar ta Python Dance II da sojin ta fara aiwatarwa tun daga ranar 15 ga watan Satumba a jihohi biyar na yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, a yanzu saura mako guda kenan su kammala wannan gudanarwar.

Sojin Kasa sun yi wata gagarumar nasara a jihar Imo

Sojin Kasa sun yi wata gagarumar nasara a jihar Imo

An samu rahoton cewa dakarun sojin yayin gudanar da aiki a yankin Obile dake karamar hukumar Egbema ta jihar Imo, su ka binciko wata maboyar wannan 'yan kugiyar ta asiri, inda suka samu muggan makamai har da AK 47 guda.

KARANTA KUMA: Amfani 7 na ruwan albasa wajen gyaran gashi

A yayin hakan dai, wasu dakarun sun yi nasarar cafke 'yan kungiyar asiri na Degbam a birnin Owerri, wanda ta bayar da sunayensu kamar haka; Onyewokechi Chiwuanya, Uchechi Agu da Esoro Chibuzor wanda rundunar ta mika su ga ofishin 'yan sanda na Egbema.

Kanal Musa ya kara da cewa, a yanzu yankunan Ohaji Egbema na jihar Imo, Aba, Ngwa da yankunan birnin Umuahia na jihar Abia, irinsu Ogured da Edda na jihar Ebonyi, tare kuma da jihar Cross River, duk sun yi lafiya kuma duka wata tarzoma wadda a da take tashi a yanzu sojin sun kwantar da ita.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel