EFCC ta damke wani mazambacin sallamammen soja da abokin zambar na sa

EFCC ta damke wani mazambacin sallamammen soja da abokin zambar na sa

- Sallamammen sojan ya na zambatar mutane ne da samar masu da aikin boge a Hukumar Sojin Kafa na Najeriya

- Rundunar Sojin Kafa ne ta kamo shi sakamakon koken mutane da ya zambata

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Hukumar EFCC ta damke wani mazambacin sallamammen soja mai suna Kabir Adamu da abokin zambar na sa mai suna Hashimu Mohammed Zakari bisa laifin zambatar mutane da aikin boge.

EFCC ta damke wani mazambacin sallamammen soja da abokin zambar na sa

EFCC ta damke wani mazambacin sallamammen soja da abokin zambar na sa

A cewar EFCC, Rundunar Sojin Kafa na Najeriya ne suka kamo Adamu sakamakon koken wadanda ya zambata da samar masu aikin boge a Hukumar Sojin Kafa na Najeriya.

DUBA WANNAN: Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

Bayan an kama shi ne ya ambaci Hashimu a matsayin abokin barnar ta sa, wanda shi ma aka yi ram da shi a Kano.

An samu I.D kad na Rundunar Sojin a hannun Adamu wanda ke dauke da sunan wani Idris Salisu amma Adamu ya sanya hoton sa makwafin hoton Idris.

Adamu ya bayyana cewa ya tsinci I.D kad dinne a wani alabe da ya sane a Jihar Legas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel