Bullar Kyandar Biri ya bayyana a Jihar Rivers

Bullar Kyandar Biri ya bayyana a Jihar Rivers

- Ana tunanin mutane 3 daga karamar hukumar Obio/Akpor na Jihar sun kamu da cutar

- Kwamishinan Kiwon Lafiya ya ce Ma'aikatar sa tana bakin kokari don hana yaduwar cutar

- Ya kuma ce a shirye su ke don yaki da cutar

Ana tunanin annoban nan na kyandar biri ya bayyana a Jihar Rivers. Kwamishinan Kiwon Lafiya na Jihar, Farfesa Princewill Chike, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fatakwal.

Bullar Kyandar Biri ya bayyana a Jihar Rivers

Bullar Kyandar Biri ya bayyana a Jihar Rivers

Farfesan ya ce ngwamnati ta killace masu dauke da cutar kuma ta sanya ido a kan su. Sunayen su shine Rumuolumeni, Eneka da Rumoimoi wanda duk 'yan karamar hukumar Obio/Akpor na Jihar.

DUBA WANNAN: Kabilar Ibo: Kungiyar Ohanaeze ta yabi matasan arewa ta yadda suka mara ma zaman lafiya baya

Kwamishinan ya kara da cewa Ma'aikatar Kiwon Lafiya tana iya kokarinta don hana yaduwar cutar. Ya sun karfafa ma asibitoci a Jihar don yakar cutar, don haka mutane su kwantar da hankalin su.

Ya kara da cewa Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta sanar da asibitocin da su kasance cikin shirin ko ta kwana. Ya kuma bayar da Lambobin da za'a kira don neman agaji na gagagawa. Wadannan lambobi su ne 08056109538, 09062277699, da 08033124314.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel