Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan cinkoson gidajen yari na kasar nan

Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan cinkoson gidajen yari na kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan irin yadda ake samun cinkoso a gidajen yari na kasar nan, inda ya ke cewa wannan abin kunya ne ga kasar nan a ce kaso 90 cikin dari na gidajen yari sun cunkushe da masu da laifi.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Jumma'a ta yau, yayin da yake karbar bakuncin wata tawaga a fadar shugaban kasar dake birnin tarayya, wannan bakin na bangaren harkokin shari'a ne wanda Babban mai Shari'a na kasa Walter Onnoghen ya jagorance su.

Ya nuna damuwarsa kwarai da aniyya, inda yake kiransu akan daukar matakai cikin gaggawa domin magance wannan cunkoso da ake fama da shi a gidajen yarin dake kasar nan.

Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan cinkoson gidajen yari na kasar nan

Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan cinkoson gidajen yari na kasar nan

Ya kuma ce, magance wannan matsala ya na da matukar fa'ida ba akan harkar shari'a kadai ba, domin kuwa hakan zai taimaka wajen inganta zamankewar mazauna gidan yari da kuma rage batar da kudi wajen yawan gyare-gyaren gidajen yari.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ba ta manta da kalubalen da harkokin shari;ar ke fuskanta ba, ya na kuma yin takaicin yadda ake kashe makudan kudi wajen harkar tsaro musamman ma a yankunan Arewa maso Gabas da yankunan Neja Delta, a maimakon inganta cigaban kasar nan.

KARANTA KUMA: An kama shugaban matan jam'iyyar APC cikin almundahanar N1.5m

Sai dai kuma ya na sa ran mutanen kasar nan za su cigaba da hakuri wajen yadda gwamnatin ta ke kokarin ta farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Yayin ya shugaban kasar ya ke yabawa bangaren shari'a na kasar nan dangane da yadda suke kokari wajen gurfanar da masu laifuka cin hanci da rashawa da ma wasu laifukan, ya kuma ce haduwar kan kasar nan da tsayuwar ta waje guda ya dogara sosai akan bangaren shari'a da kuma hukumar 'yan sanda.

Shi kuwa jagoran tawagar mai shari'a Onnoghen ya yiwa Ubangiji godiya kan yadda shugaban kasar ya samu waraka, ya kuma tabbatarwa da shugaban kasar cewa za su ci gaba da tsayawa tsayin daka don ganin sun yi wa kasar nan abin da take bukata.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel